
Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ‘Super eagles’ zata kece raini da kasashen Argentina da Iceland da kuma Kurwatiya a rukuni na D, a gasar cin kofin duniya da za’a kara a shekarar badi a kasar Rasha.
A wani kayataccen biki da aka gudanar a fadar Gwamnatin Rasha dake Kremlin a babban birnin kasar Moskow, an zabi Najeriya inda zata kara da kasashen Argentina da Kurwatiya da kuma kasar Iceland a matsayin rukuni na D.
Idan ba’a mance ba, a baya bayan nan, Najeriya ta kara a wasan sada zumunci da kasar Argentina, inda ta doke Argentina din da ci 4 da 3, wanda masu fashin baki suke ganin waccan nasara da najeriyar ta samu,ka iya baiwa ‘yan wasan kwarin guiwar sake doke Argentina a gasar cin kofin duniyar da za’a yi a Rasha.
Rukuni na A: Rasha, Saudiyya, Masar, Urguay
Rukuni na B: Portugal, Sifaniya, Moroko, Iran
Rukuni na C: Faransa, Austeraliya, Peru, Denmark
Rukuni na D: Najeriya, Argentina, Icelan, Kurwatiya
Rukuni na E: Barazil, Siwizalan, Kosta-Rika, Sabiya
Rukuni na F: Jamus, Meziko, Siwidin, Jamhuriyyar Koriya
Rukuni na G: Beljika, Fanama, Tunusiya, Ingila
Rukuni na H: Polanda, Senegal, Kwalambiya, jafan