
Yayin da rashin tsaro ke ci gaba da taɓarɓarewa a yankin Arewacin Nijeriya da ma wasu sassa na ƙasar, hankalin kowa ya koma ga rungumar addu’a domin Allah Ya kawo ɗauki.
Ita ma Ɗariƙar Ƙadiryya ba a barta a baya ba, inda Shugaban ta na Afirka, Sheikh Ƙaribullah Nasiru Kabara, ya jagoranci addu’a ta musamman domin zaman lafiya a ƙasar nan.
A yayin taron addu’ar, wanda a ka gudanar a yau Lahadi a Gidan Ƙadiriyya a Jihar Kano, Sheikh Ƙaribullah ya yi kira ga al’ummar ƙasa da su dage da addu’a domin Allah Ya yaye masifar rashin tsaro da ke damun al’umma.
A cewar sa, kashe-kashen al’umma da a ke yi, musamman a Arewacin Nijeriya, abu ne da ke damun kowa da kowa, inda ya baiyana cewa dole sai al’umma sun koma ga Allah sun gyara mu’amalolin su sannan za a samu sauƙin lamarin.
Ya kuma yi kira ga al’umma da su rungumi addu’a su riƙa yi ka’in-da-na’in domin Allah Ya kawo ɗauki.
Shugaban ya baiyana cewa “duk wani wanda ya ke shirya wannan kashe-kashen, ko wanda ya ke ɗaukar nauyi, da ma masu yin kashe-kashen, dukkan su mun ce musu, ‘Allah Ya fi su’.
“Sai mu dage da addu’a da kuma karanta Hasbunallahu wa ni’imal Wakil, Salatin annabi da kuma istigfari a kowacce rana. Idan mu ka ɗauki kamar tsawon watanni 3 mu na yi, in sha Allah za mu samu sauƙi,” in ji Ƙaribullah.
Ya ƙara da cewa addu’a irin wannan ta samo asali ne tun lokacin Annabi Muhammad (SAW), yayin da duk wata musiba ta afku, Annabi ya na bada umarnin a fita a roƙi Allah.
“A na so ma kowa ya fita yin addu’ar. Matasa, tsofaffi, mata da yara kowa ya fita domin ba a san bakin wa Allah zai karɓi addu’ar sa ba,” in shi.
Sheikh Ƙaribullah ya ce a riƙa karanta salati a ƙalla 100 a rana, Hasbunallahu wa ni’imal Wakil 45 sai kuma istigfari a yi ta yi gwargwadon iko.