Home Labarai Rashin tsaro: Mun damu da ɓatan sama da mutane dubu 25 a Nijeriya — ICRC

Rashin tsaro: Mun damu da ɓatan sama da mutane dubu 25 a Nijeriya — ICRC

0
Rashin tsaro: Mun damu da ɓatan sama da mutane dubu 25 a Nijeriya — ICRC

Kwamitin Agaji na Kasa-da-ƙasa, ICRC, ya bayyana damuwa kan ɓatan ƴan Nijeriya har sama da dubu 25 sakamakon rashin tsaro a ƙasar.

Dangane da wannan batu ne ICRC ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana shirinsa na gudanar da taro da masu ruwa da tsaki a yau Talata domin yin nazari kan yadda za a ɓullo wa lamarin.

A cikin sanarwar da ya fitar a a jiya Litinin, ICRC Nigeria, ya ce taron na neman wayar da kan jama’a, samar da hanyoyin haɗa hannu waje guda tare da samar da hanyoyin magance lamarin.

Sanarwar ta kuma kara da cewa taron zai kuma samar da hanyoyin da za a bi wajen gudanar da aiki tare, tare da tattauna batutuwan da suka fi muhimmanci da kuma shirin aiwatar da ayyukan tallafawa iyalan wadanda suka ɓatan.

A cewar ICRC, dubban iyalai na ci gaba da neman mutane sama da 25,000 da suka bata sakamakon rikicin yankin arewa maso gabas.

Yayin da yake jaddada cewa ba za a manta da wadanda suka bata ba, wani jami’in kwamitin na ICRC, Kouame Adjoumani, ya ce “duk wanda ya bata, ƙarƙashin sa a kwai mutane da dama da ke fama da kunci da rashin tabbas na rashin sanin makomarsu da kuma inda wani masoyi ya ke”.

Ya kara da cewa, “Iyalan wadanda suka bata suna fuskantar matsalolin tattalin arziki, zamantakewa, da shari’a gaba daya-kuma ba za su iya sake gina rayuwarsu ba har sai an shawo kan wadannan kalubale.