
Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Katsina ta ce ta kama masu laifi 999 da su ka aikata kaifuka iri-iri har 608 a shekarar 2021 da mu ke bankwana da ita.
Kakakin rundunar, SP Isah Gambo ne ya baiyana hakan a madadin Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, AIG Sunusi Buba a yayin taron manema labarai na ƙarshen shekara a Katsina.
Gambo ya yi bayanin cewa, daga cikin waɗanda a ka kama, an kai 874 kotuna daban-daban a jihar.
Ya ƙara da cewa an kama ƴan fashi da makami 157, inda a ka kai 145 kotu, inda kuma a ke bincikar 12 daga ciki.
Kakakin ya ƙara da cewa adadin masu garkuwa da mutane 65 ne a ka kama shekarar da mu ke bankwana da ita, inda ya ƙara da cewa an kai 63 kotu, 2 kuma suna ƙarƙashin bincike.
“Masu satar shanu 244 a ka kamar tsawon shekarar, inda 230 suna kotu, ana kan binciken 14 da ga cikin su,”
Sai dai kuma rundunar ta ce ta rasa jami’an ta 5, inda ta hallaka ƴan fashin daji 38 a fafatawa daban-daban.
“A shekarar da mu ke bankwana da ita, mun ƙwato dabbobin gida 1, 243 da su ka haɗa da shanu 800, tumaki 352, awaki 24 sai kuma baki guda 1.