Home Labarai Rashin tsaro: Mutane na ci gaba da tserewa a wasu yankunan Zamfara

Rashin tsaro: Mutane na ci gaba da tserewa a wasu yankunan Zamfara

0
Rashin tsaro: Mutane na ci gaba da tserewa a wasu yankunan Zamfara

 

Gwamman mutane ne rahotanni ke cewa na ci gaba da tserewa gidajensu a yankunan Bukkuyum da Anka a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, yayin da ‘yan fashin daji suka mamaye ƙauyukan yankin.

Wasu da suka tsere zuwa garin Nassarawa Burƙullu sun shaida wa BBC cewa ɗaruruwan ‘yan fashin daji ne a kan babura ke ci gaba da ƙone-ƙone da kashe-kashe har ma da sace mata zuwa daji.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da mutanen Gudu a jihar Sokoto, ke ci gaba da alhini bayan sace wasu matan aure ranar Alhamis a kan hanyarsu ta komawa gida.