
Ma’aikatar kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin-Duniya, UNCHR ta baiyana cewa rashin tsaro a arewa-Maso-Yammacin Nijeriya ya tilastawa mutane 11,500 gudun hijira zuwa Ƙasar Nijar a watan Nuwamba.
Kakakin UNCHR, Boris Cheshirkov ne ya baiyana haka a wata ganawa da manema labarai a Geneva a yau Juma’a.
Ya ce ” mu na cikin damuwa da tashin hankalin da ke faruwa a arewa-Maso-Yammacin Nijeriya kuma yanayi ne da ya ke buƙatar haɗa hannu guda wajen samar da zaman lafiya.
“Yawancin sabbin zuwan sun samu matsuguni a ƙauyuka 26 a cikin Nijar ɗin. Yawancin ƴan gudun hijirar mata ne da ƙananan yara. Saboda haka muna buƙatar taimako mai ƙarfi domin sauƙaƙa rayuwar al’umma,”