
Real Madrid ta samu tabbacin ɗaukar Kylian Mbappe a kyauta a karshen kakar wasanni ta bana, in ji jaridar wasanni ta AS.
Mbappe, ɗan shekara 22, ya yanke cewa ba zai sabunta kwantaraginsa da PSG ba, wacce a ƙarshen kakar bana za ta ƙare.
A yanzu haka, rahotanni sun baiyana cewa tuni dai Madrid ta fara shirye-shirye na ɗaukar Mbappe ɗin.