Home Wasanni Real Madrid za ta wafce Jose Mourinho daga hannun Manchester United

Real Madrid za ta wafce Jose Mourinho daga hannun Manchester United

0
Real Madrid za ta wafce Jose Mourinho daga hannun Manchester United

Daga Hassan Y.A. Malik

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya fara tattaunawa da kungiyar Real Madrid a wani salo na kome zuwa ga kungiyar da ya taba horarwa a baya kamr dai yadda jaridar kwallon kafa ta Ok Diario ta rawaito.

Jaridar ta Ok Diario ta wallafo cewa tuni dai wata tawaga ta Real Madrid din ta tuntubi wakilan Mourinho kan batun ko zai iya barin Manchester United ya koma Real Madrid da aiki.

Wannan kuwa ya bayan gurbin da Zinedine Zidane ya bari ne bayan ya ajiye aiki a wani yanayi na bazato ba tsammani bayan da kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai sau 3 a jere a karkashin kulawarsa.

Mauricio Pochettino, Antonio Conte, Jurgen Klopp, Joachim Low na daga cikin wadanda kungiyar ke hange a matsayin magada ga Zidane, sai dai kwatsam kuma aka jiyo kungiyar ta sanya sunan Mourinho a matsayin wanda kungiyar ke muradin ya jagoranceta.

An ruwaito cewa shugaban hukumar gudanarwar kungiyar, Florentino Perez ne ya bukaci da lalle a nemo Mourinho ya karbi Madrid din wanda dama ya taba rike kungiyar tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013.

Dama dai a watan da ya gabata, jaridar Daily Telegraph ta rawaito cewa wasu jiga-jigai a Manchester United sun nuna rashin jin dadinsu kan salon yadda Mourinho ke tafiyar da kungiyar tare da ja masa kunne kan ya canja salonsa a kakar wasa mai zuwa.

A saboda haka, wannan kaka ita ce kaka mafi mahimmaci ga Mourinho a Manchester United, inda zai dada tabbatrwa da wadanda ke da shakku akansa cewa har yanzu fa zai iya canja al’amura.

Tuni dai Mourinho ya kammala daukar ‘yan wasa biyu: Fred daga Shaktar akan fam miliyan 52 da Diogo Dalot daga Porto akan fam miliyan 17.4