Home Lafiya Rigakafin maleriya ta ƙananan yara ce ba manya ba — Gwamnatin tarayya

Rigakafin maleriya ta ƙananan yara ce ba manya ba — Gwamnatin tarayya

0
Rigakafin maleriya ta ƙananan yara ce ba manya ba — Gwamnatin tarayya

 

 

 

Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin zazzabin cizon sauro ta farko da hukumar lafiya ta duniya WHO ta amince da ita , za a yi ta ne a karo huɗu-hudu ga jarirai ƴan watanni 5 ne kaɗai ba manya ba.

WHO ta kuma ce allurar za ta yi tasiri a kan muggan kwayoyin cutar ta maleriya, musamman wacce ta Afirka kuma ba don manya aka yi ta ba.

Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a jiya Talata a Abuja yayin wani taron haɗin-gwiwa na ministoci don tattaunawa kan ci gaban da ake samu a yaƙi da COVID-19 da ci gaba a bangaren kiwon lafiyar kasar.

Rahoton zazzabin cizon sauro na duniya na shekarar 2021, WMR 2021, ya nuna cewa Najeriya na ɗaukar kashi 27 cikin 100 na masu fama da cutar zazzabin cizon sauro a duniya da kuma kashi 32 cikin 100 na mace-macen zazzabin cizon sauro a duniya.

Ministan ya ce ƴan Nijeriya miliyan 57 ne ke kamuwa da cutar a kowace shekara da kuma mutuwar kusan 100,000 a shekara.

“An kuma kiyasta kusan kashi 60 cikin 100 na dukkan marasa lafiya da kuma kashi 30 cikin 100 na duk asibitocin da ake kwantar da su a fadin kasar nan suna fama da zazzabin cizon sauro”, in ji shi.

Mista Ehanire ya ce har yanzu ana ci gaba da nazari kan allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro inda ta farko da aka sani na rage hadarin kamuwa da zazzabin cizon sauro da kashi 40 cikin 100 na yara a Afirka a shekarar 2020