
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da ɓarkewar wani mummunan rikici tsakanin Manoma da Makiyaya a kudancin Numan dake jihar Adamawa.
Ganau ya tabbatar ya tabbatar da ganin gawarwaki masu dumbin yawa yashe, yayin da da dama suka tsre suka bar gidajensu.
Wannan harin dai ance, na ramuwar gayya ne da Fulani suka kai domin daukar fansar, mutanan da aka kashe a Numan ‘yan kwanakin da suka gabata, wanda ‘yan kabiilar Bachama suka kai.
A lokacin da yake tabbatar da faruwar wannan al’amari, Othman Abubakar, yave rikicin ya faro ne daga kauyen Dong a karamar hukumar Demsa, sakamakon rashin fahimtar juna tsakanin wasu manoma da fulani masu kiwo.
“Ya zuwa yanzu dai, tuni aka jibge tarin jami’an tsaro a dukkan sassan da rikicin ya auku, domin dawo da duka da oda a yankunan”
“Ba zan iya tabbatarwa ko wannan rikicin yana da alaka da wanda ya faru a kwanakin baya ba, dan daukar fansar ko kuma a’a”
Da yawan mutunan garin ‘yan asalin kabilar Bachama duk sun tsre sun bar gidajensu, domin tsira da rayukansu, Gregon Daniel daya ne daga cikin mutanan da suka tsere, yace, “an bankawa gidansa wuta, Fulani sun tayar da garuruwanmu na Lawaru da Dong a karamar hukumar Demsa gabaki daya”
“Fulani ne masu yawa, suka zo suka yiwa kauyen namu kawanya, inda suka hau kisa babu ji babu gani, sannan suka cinnawa gidaje da dama wuta”
“Yanzu haka maganar nan da nake, wannan rikici yana cigaba, gidaje da dama a garuruwanmu na ci da wuta, yayin da mata da yara suke guduwa daji domin samun tsira”