Home Siyasa Rikicin APC: Ɓangaren ganduje ya sake shan kaye a kotu

Rikicin APC: Ɓangaren ganduje ya sake shan kaye a kotu

0
Rikicin APC: Ɓangaren ganduje ya sake shan kaye a kotu

 

A yau Alhamis ne wata babbar Kotu a Abuja, ta yi watsi da wasu roƙo guda biyu da ɓangaren Ganduje na jam’iyar APC ya shigar gaban ta.

A ranar 30 ga watan Nuwamba ne Mai Shari’a Hamza Muazu ya biyawa ɓangaren Shekarau dukkanin roƙon su, in da su ke iƙirarin cewa tsarin Ganduje bai yi zaɓen shugabannin jam’iya na jiha ba.

Da jin haka, sai ɓangaren Ganduje ya garzaya kotu, inda ya nemi kotu ta tsayar da sauraron ƙarar ta su Shekarau sannan kuma ta yi watsi ƙorafin su a kan zaɓen shugabannin jam’iya na jiha.

Da ya ke yanke hukunci a ka ƙorafin na su Ganduje a ranar 17 ga Disambar 2021, alƙalin ya yi watsi da rokon na su ɓangaren Ganduje, inda ya ci tarar su Naira miliyan 1 sakamakon batawa ɗaya tsagin lokaci.

Amma, kafin kotun ta yanke hukunci a kan roƙo guda biyun da su Shekarau su ka yi mata, sai tsagin Ganduje ya ɗaukaka ƙara, su ka kuma haɗa da takardun roƙon nasu da su ka shigar a babbar kotun ta Abuja.

Da ya ke hukunci a kai a yau Alhamis, Alƙalin ya yi watsi da roƙon na ɓangaren Ganduje a bisa hujjar cewa sun kai takardun roƙon nasu zuwa kotun ɗaukaka ƙara, inda ya ce ba ta da hurumin ta saurari ƙarar.

A na tsammanin kotun ɗaukaka ƙarar za ta yanke hukunci kan ƙarar a cikin kwanaki 60.