Home Siyasa Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

0
Rikicin APC: Sanata Abdullahi Adamu ya bada haƙuri

 

 

 

Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyar APC na ƙasa, ya bada haƙuri a kan rikicin da ya kunno kai a kwanan nan.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa kwanaki uku da su ka gabata ne dai wasu masu riƙe da muƙamai a APC, Mataimakin Shugaban Jam’iya, Arewa-maso-Yamma, Mallam Salihu Lukman da takwaransa na Kudu-maso-Yamma, Isaac Kekemeke su ka zargi Adamu da ajiye su a gefe a al’amuran jam’iyyar ba tare da yi da su ba.

Sun zargi Adamu da yin abubuwa da dama waɗanda ba su dace ba a shugabancin jam’iyar, inda su ka nuna ɓacin ransu kan yadda ya ke ɗaukar matakai shi kaɗai ba tare da aiki tare da sauran nataimakansa ba

Sai dai kuma rahotanni sun baiyana cewa, a wata ganawa mai tsawo da ya yi da shugabanni da masu ruwa da tsaki na APC a Abuja a jiya Laraba, Sanata Adamu ya fito fili ya amsa laifinsa.

Hakazalika Sanata Adamu ya baiwa duk wanda a ka ɓata wa haƙuri, inda ya yi alƙawarin gyara kurakurensa da kuma tafiya da kowa a wajen tafiyar da al’amuran jam’iyar.