
Daga Hassan Y.A. Malik
Rahotanni sun bayyana cewa mai mallakar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich tuni ya fitar da wanda zai gaji kovcin kungiyar, Antonio Conte da zarar kakar kwallon kafa ta badi ta kama.
Dangantaka dai ta yi tsami tsakanin hukumomi a kungiyar Chelsea da Antonio Conte sakamakon rashin fahimtar juna da akan abubuwa da suka hada da tsarin saye da sayarwar ‘yan wasa na kungiyar da kuma yadda Conte ke gudanar da danganataka tsakaninsa da ‘yan wasan kungiyar.
Haka kuma Conte bai yi wani abin a zo a gani ba a kakar wasa ta bana bayan da ya dauki kofin gasar firimiya a bara.
Tuni dai Abramovich ya yanke hukuncin sauya Conte da Mauricio Pochettino na Tottenham kuma har shi Pochettinon ya san da wannan shiri na Abramovich.
Sai dai Conte mai shekaru 48 ya bayyana a fili cewa shi fa har yanzu yana da ragowar shekara guda na kwantiraginsa da Chelsea kuma a shirye yake da ya kammala wa’adinsa.