Home Wasanni Ronaldo baya goyon bayan Real Madrid ta sayo Neymar

Ronaldo baya goyon bayan Real Madrid ta sayo Neymar

0
Ronaldo baya goyon bayan Real Madrid ta sayo Neymar

Daga Hassan Y.A. Malik

Rahotanni na nuna cewa Cristiano Ronaldo na Real Madrid baya goyon bayan kungiyarsa da ta sayo Neymar Jr daga PSG a kakar saye da sayarwar ‘yan wasa da za a shiga nan ba dadewa ba.

Neymar dai ya kasance dan wasan da Real Madrid suke sha’awar dauka, wanda tuni ya ke burge shugaban mjalisar gudanrwar Real Madrid, Florentino Perez.

Neymar mai shekaru 26 ya koma PSG daga Barcelona a wani ciniki na fam miliyan 200 da ya sanya ya zama dan wasan da ya fi kowane dan wasa tsada.

Sai dai rahotanni daga jaridar Don Balon na cewa Ronaldo na kokarin yin duk mai yiwuwa don ganin ya dakatar da batun kawo Neymar Real Madrid.

Shi ma mai horas da kungiyar Real Madrid din, Zinadne Zidane  baya da sha’awar yin aiki da Neymar domin wai ba zai dace da tsarin fasalin wasanninsa ba.