
Daga Abba Wada Gwale
Dan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ya bada umarnin a siyar da kyautar da yaci ta gwarzon dan kwallon duniya (Ballon d’Or) domin a bayar da kudin sadaka ga wata gidauniya wadda take tallafawa yara ƙanana domin cimma burinsu.
Ronaldo ya fara lashe kyautar ɗan ƙwallon duniya ne a shekara ta 2008 lokacin da yake Manchester United, sannan kuma ya sake lashe kyautar sau uku bayan ya koma Real Madrid a shekarar 2009 akan kuɗi fam miliyan 80.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da dan wasan yake bada taimako ga ƙungiyoyi da kuma mutane daban-daban domin taimakawa masu buƙatar taimako.
A hirar da yayi da manema labarai bayan ya bada sanarwar siyar da kyautar tasa, Ronaldo, mai shekaru 32 yace ya yi kewar Manchester United sai dai ya ce bai yi danasanin barin ƙungiyar ba tunda ya lashe kofuna a Real Madrid din bayan ya koma.
Ronaldo dai ya ci gasar Premier ta ƙasar Ingila sau uku sai kofin ƙalubale sau daya da kofin zakarun turai kafin daga baya kuma ya koma Real Madrid inda nanma ya lashe gasar La Liga guda biyu, sai kofin Copa del Rey guda biyu da kuma gasar zakarun Turai guda uku.
Ya kuma taimakawa ƙasarsa ta Portugal ta lashe kofin Nahiyar Turai a kakar wasan data wuce bayan da suka doke mai masauƙin baƙi ƙasar Faransa.