
A jiya Litinin ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya umarci jami’an tsaro na SSS, da su kulle shi a otel na tsawon awanni 48 a jihar.
Mista El-Rufai ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2013 lokacin da ya je jihar a matsayin jami’in sanya ido na jam’iyyar APC, domin shaida zaben maimai na gwamnan jihar Anambra.
El Rufa’i ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin hadin gwiwa na yankin Kaduna ranar Litinin tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Tinubu da Obi sun yi wa shugabannin Arewa jawabi game da tsare-tsare da kudirorinsu ga yankin.
Ko da ya ke El-Rufai ya ce yana da dukkanin jami’an tsaro a hannunsa a matsayinsa na gwamnan jihar Kaduna a yanzu domin ya rama zaluncin da aka yi masa, amma ba zai rama mugunta da mugunta ba.
“A shekarar 2013 na je jihar Anambra a matsayin jami’in jam’iyyar APC domin shaida zaben fidda gwani na gwamna. Bakonku, Peter Obi, shine gwamna a Lokacin. Ya sa a ka tsare ni na tsawon awanni 48 a dakin otal di na.
“Yanzu ni ne gwamnan jihar Kaduna. Kuma yana zuwa Kaduna, ban da ’yan sanda da SSS, ina da shiyya-shiyya guda daya na rundunar sojojin Nijeriya a nan idan ina bukatar kamawa da tsare kowa. Amma mu ’yan Arewa ne, muna da wayewa, ba ma yin haka.”