
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce yanzu haka ‘yan Najeriya na cin shinkafar gida bayan rufe iyakokin kasar.
Buhari ya yabawa manoman kasar nan kan yadda suke noman shinkafa da sauran kayan abinci.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne a jiya Juma’a a Katsina, wajen wani taro da ya gudanar da zaɓaɓɓun shugabannin Ƙananan Hukumomin jihar.
Shugaban ya bayyana jin daɗinsa da yadda manufofin gwamnatin sa na noma su kai aiki yadda ya kamata.
Buhari ya ce yana da kyakkyawar fahimtar al’ummar Nigeria, haka tasa suka rungumi tsare-tsarensa na noma.
“Na ce dole ne mu noma abin da muke ci kuma mu ci abin da muka noma. Wannan kasa ce da ta taɓa dogaro da shinkafar waje a baya.
“Mun rufe iyakar mu don hana shigo da shinkafar waje. hakan tasa na ce me ya sa ba za mu cin shinkafar mu ta gida Nijeriya ba, kuma ga shi nan bisa tsarin da muka yi, yanzu haka‘yan Nijeriya suna cin shinkafar gida.” Inji Buhari
Buhari ya kara da cewa aiwatar da tsarin asusun bai daya na Treasury Single Account (TSA) ya taimaka wa gwamnati wajen dakile aiyukan jami’an gwamnati marasa kishin kasa.