
Reshen ɗalibai na Gamayyar Ƙungiyoyin Farar hula na Arewa, CNG-SW sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewa in har gwamnatin taraiya da ASUU ba su sansata an janye yakin aikin da sunke yi ba.
Ɗaliban sun kuma yi barazanar rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa a Nijeriya.
CNG-SW ta yi wannan barazana ne a wata takardar bayanin bayan taro, wanda koodinetocin kungiyar na jihohi 19 su ka gudanar a yau Juma’a a Kanno.
Da ya ke karanta takardar ga manema labarai, Koodinetan kungiyar na ƙasa, Jamilu Charanchi ya ce CNG-SW ta cika da damuwa bisa yadda yajin aikin ASUU da na kwalejojin ilimi ya ci tira.
A cewar ƙungiyar yajin aikin ya jefa ƴaƴan talakawa cikin wata irin mawuyaciyar rayuwa.
CNG-SW ta ƙara da cewa tuni ta ɗauki gaɓaran rubuta ƙorafi ga sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an gwamnati da jami’an tsaro a kan su saka baki a kawo karshen yakin aikin.
“Idan haka ba ta samu ba, to za mu rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin ƙasa da manyan titunan Arewacin Nijeriya.
“Za kuma mu rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa,” in ji CNG-SW.