Home Labarai Rugujewar gini ta hallaka ƴan uwa ciki ɗaya su 2 a Kano

Rugujewar gini ta hallaka ƴan uwa ciki ɗaya su 2 a Kano

0
Rugujewar gini ta hallaka ƴan uwa ciki ɗaya su 2 a Kano

 

 

 

Wasu ƴan uwa biyu ƴan ciki ɗaya, ɗan shekara 15 da ɗan shekara 11 sun mutu sakamakon rushewar gini a Kano a ranar Juma’a.

Sai dai kuma an ceto babban yayansu, mai shekaru 17 da ransa.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a jiya Asabar a Kano, inda ya ce gidan yana kofar Mata, Hauren Gadagi a Kano.

“Mun sami kiran waya na gaggawa da misalin karfe 10:50 na dare daga wani Jamilu Salisu Zango, cewa gidan na zama mai kafa 50 x 40 ya ruguje daga saman bene.

“Mun aika da tawagarmu zuwa wurin da lamarin ya faru kuma an fito da ’yan’uwan su uku daga cikin ɓaraguzan. Biyu daga cikinsu ba su hayyaci ba,” inji shi.

Abdullahi ya kara da cewa an garzaya da waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin Murtala Muhammad na musamman domin kula da lafiyarsu inda likitoci suka tabbatar da mutuwar ‘yan uwan ​​biyu.

Ya ce an mika gawarwakin ga ƴan sanda a ofishin ƴan sanda na Kofar Wambai, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.