
Rundunar Ƴan Sanda ta ƙasa reshen jihar Kano ta sha alwashin haɗa hannu da ƙungiyar kasuwar hada-hadar wayoyin hannu ta jihar domin daƙile matsalar sace-sace da ƙwace-ƙwacen wayoyi a jihar.
Kwamishinan Ƴan Sandan jihar Kano, Sama’ila Dikko ne ya tabbatar da hakan a lokacin da ƙungiyar ta kai masa ziyara da kuma bashi lambar girma a ofishinsa.
Kwamishinan ya ce ya yi matukar farin ciki bisa yadda kungiyar tayi kudirin haɗa hannu da rundunar domin ganin an daƙile ta’adar sace-sacen wayoyi, musamman a wannan lokaci da lamarin ya addabi al’ummar jihar Kano.
Samaila Dikko yace kofarsu a bude take wajen yin mu’amala da kungiyar duba da yawan kasuwannin siyar da wayoyin dake Kano, inda yace kungiyar zata taka rawar gani wajen zaƙulo ɓata-garin ta hanyoyin daban-daban.
Tun da fari, a jawabinsa, Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin hada-hadar Wayoyin hannu ta jihar Kano, Alhaji Ahmad Tijjani usman yace Kwamishinan yan sandan jihar Kano ya gayyaci kungiyar domin tattaunawa da ita kan zargin da ake yiwa yan kasuwar wayoyin hannu.
yace ana zargin ana haɗa kai da masu sayar da wayoyin domin sayar da wayoyin da aka sato ko kwatowa, inda ya ce ya ce wannan zargi ba haka yake ba domin sums suna iya bakin kokarisu don ganin basu sayi wayar da aka sato ko aka kwato ba.
Shugaban kungiyar yace bayyana cewa zasu bada gudunmowarsu don kawar da wannan dabi’a da matasa suke yi a fadin jihar nan.
Shugaban yace kungiyar ta Samar da cikakken kwamiti na musamman domin bibyar masu shigowa kasuwannin wayoyin hannu domin sayar da wayoyin da suka kwata ko sata domin Idan ba’a sayan wayoyin dole barayin su daina satowa.
Ya kuma lambobin karta-kwana ga duk wanda a ka sace wa ko kwace wa waya domin gano waɗanda su ka aikata cikin gaggawa.
Lambobin sune ; 08065416459 ko 08039725508 ko kuma kanomofsa@gmail.com.