
A jiya Asabar ne bataliya ta 241 ta Rundunar Sojin Ƙasa ta kori John Gabriel da Adamu Gideon, mai muƙamin Lans Kofral da ake zargin sun kashe wani malamin addinin Muslunci, Sheikh Goni Aisami a Yobe.
Babban Kwamandan Bataliyar, wacce ta ke Nguru, Yobe, Ibrahim Osabo ne ya bayyana haka ga manema labarai, jim kadan bayan an cire wa waɗanda ake zargin kakinsu a Nguru.
Sai da a ka rage wa waɗanda ake zargin mukami daga Lans Kofral zuwa sojoji masu zaman kansu kafin kuma daga bisani a kore su.
“Dukkan ku kuna sane da abin da ya faru mako guda da ya gabata inda jami’an nan namu biyu da ke aiki a wannan bataliya su ka fita su ka aikata wannan ta’asa, sannan jami’an ƴan sandan Nijeriya suka kama su.
Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki da ya bamu ikon yin abin da ya dace. Mun fara bincike daga sashen ƴan sandan soja tare da ƴan sandan Nijeriya.
“Sakamakon binciken ne ya sanya mu ka fara hukunta waɗanda ake zargi, inda yanzu an kore su a hukumance daga rundunar sojojin Najeriya,” in ji Osabo.
Ya kuma kara da cewa za a mika su a hukumance ga hukumar ƴan sandan Najeriya domin fuskantar shari’a.