
Rundunar sojin ƙasa ta tabbatar da kisan Birgediya-Janar Dzarma Zirkushu, kwamandan runduna ta 28 da ke Chibok a hannun ƙungiyar ya’n ta’adda, ISWAP.
Ƴan ta’addan sun kashe janar ɗin ne tare da wasu sojoji uku a kan hanyar su ta zuwa kai ɗauki a ƙauyen Bungulawa da ke Askira Uba.
A sanarwar da kakakin Rundunar Sojin-ƙasa, Onyeama Nwachukwu ya ce dakarun sun samu nasarar kare yankin su sannan sun lalata kayan yaƙin ISWAP ɗin a yayin fafatawar.
“Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabas mai suna Operation Haɗin Kai ta ragargaza ƴan ƙungiyar ISWAP a fafatawar da mu ka yi da su a Ƙaramar Hukumar Askira Uba da ke Jihar Borno.
“A halin yanzu ma da a ke fitar da wannan sanarwar, ana nan ana ƙazamin faɗa da ƴan ta’addar, in da dakarun su ka samu ɗauki daga jiragen yaƙin OPHK inda su ka ragargaza have destroyed kayan yaƙin ƴan ta’addan da su ka haɗa da A-Jet guda biyar, A-29 guda biyu, Dragon combat vehicles da kuma motoci masu ɗaukar jigida guda tara.
“Abin takaici, Birgediya-Janar Dzarma Zirkushu da wasu sojoji uku sun rasa rayukansu a yayin fafatawar bayan da su ka taka gagarumar rawa wajen kaiwa dakarun mu ɗauki mu ka bawa ƴan ta’addan kashi sannan mu ka kare yankin mu.
“Tuni mu ka sanar da iyalan mamatan.
“Shugaban Sojojin Ƙasa, Laftanal Janar Faruk Yahaya ya taya iyalai da ƴan uwan sojojin da su ka rasa ransu. Ya kuma bawa dakarun umarnin su ci gaba da jajircewa da zage dantse wajen bin ragowar ƴan ta’addan da ke tserewa domin kawo ƙarshen su gaba ɗaya,” in ji sanarwar.