Home Labarai Rundunar sojin-ƙasa ta yarda cewa sojoji na ta ajiye aiki, amma ta baiyana dalili

Rundunar sojin-ƙasa ta yarda cewa sojoji na ta ajiye aiki, amma ta baiyana dalili

0
Rundunar sojin-ƙasa ta yarda cewa sojoji na ta ajiye aiki, amma ta baiyana dalili

Rundunar Sojin-ƙasan Najeriya ta ce yin ritaya na ƙashin kai da sallamar ma’aikata abu ne na yau da kullun kuma ya yi daidai da ka’idojin da aka gindaya kamar yadda ya ke kunshe a cikin Ka’idoji da Sharuɗɗan Aikin soja, wanda ya shafi manya da kananan sojoji.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Maj.-Gen. Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja.

Nwachukwu ya caccaki labarin da wasu kafafen yada labarai suka buga kwanan nan, inda su ka rawaito yadda sojoji ke barin aiki saboda cin hanci da rashawa, rashin walwala da makamantansu.

Ya ce rahotannin ba wai yaudara ce kawai ba, har ma da yunkurin shuka ɓatanci da kiyayya tare da bata sunan kishin ƙasa na ma’aikata da mutuncin sojojin Nijeriya.

A cewarsa, yana da matukar muhimmanci a fayyace cewa aikin sojan Najeriya, kamar yawancin sojoji a duniya, na ganin dama ne ba.

“Saboda haka, wannan ya na nufin cewa soja na da damar barin aiki a duk sanda ya ga dama kuma mu ma haka ya ke a rundunar sojin-ƙasa.

“Ma’aikata suna da ‘yancin ajiye aiki daga lokaci zuwa lokaci bisa ga ka’idojin da aka gindaya

“barin aiki a rundunar sojojin Najeriya abu ne na yau da kullun kuma da ya yi daidai da tsarin da aka gindaya,” in ji shi.