Home Labarai Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sabbin sojoji 4,000

Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sabbin sojoji 4,000

0
Rundunar Sojin Ƙasa ta yaye sabbin sojoji 4,000

 

Rundunar Sojin Ƙasa ta Nijeriya, wacce a ka fi sani da ‘Nigerian Army’ ta yaye sabbin matasan sojoji guda 4,000.

Da ya ke jawabi a yayin bikin yaye sabbin sojojin, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanal Janar Faruk Yahya, ya hore su da su sanya buƙatun ƙasar nan a sama da buƙatunsu na kashin kan su.

Ya kuma yi kira a gare su da su zama masu nuna ƙwarewa da bin ƙa’idar aiki a yayin da su ke aiki.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a yayin bikin yaye sojojin karo na 81 a defo ɗin rundunar sojin ƙasa da ke Zariya, Jihar Kaduna a jiya Asabar.

Da ya ke taya sabbin sojojin murnar kammala horo, Shugaban ya baiyana cewa horon da a ke yiwa sabbin ƙananan sojoji wani cikamaki ne na umarnin shalkwatar sojin ƙasa ta ƙasar nan da ya ke kan doron horo na samar da kwararrun dakarun sojin ƙasa domin cimma ƙudurin kare ƙasar nan.

A wata sanarwa da kakin rundunar ya fitar, Onyema Nwachukwu, Shugaban ya ce bikin yaye sojojin wani gagrumi ne a tarihin horo na rundunar yayin da ta sake horar da sabbin zaƙaƙuran sojoji da za su taimaka wajen kare ƙasar nan.