Home Labarai Rundunar sojin sama ta fara bincike kan zargin kisan matashi da jami’in ta ya yi a Kano

Rundunar sojin sama ta fara bincike kan zargin kisan matashi da jami’in ta ya yi a Kano

0
Rundunar sojin sama ta fara bincike kan zargin kisan matashi da jami’in ta ya yi a Kano

Rundunar sojin sama, NAF, ta ce ta fara bincike kan zargin da ake yi na cewa wani sojan sama ya kashe wani matashi a jihar Kano.

Daily Trust ta rawaito cewa mazauna yankin Gwagwarwa da ke karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano sun bukaci a yi musu shari’a kan zargin kashe wani matashin, Yusuf Shuaibu dan shekaru 23 da haihuwa.

Marigayin, wanda yake aiki a matsayin mai aikin goge-goge a asibitin sojojin saman Najeriya da ke Kano, an bayyana cewa ya samu munanan raunuka a hannun jami’in sojan mai suna Oga Aminu.

Shu’aibu Bala, mahaifin marigayin ya ba da labarin abin da ya faru.

Ya ce, “Bayan ya kammala aikin dare, Yusuf yana shirin komawa gida sai Oga Aminu ya umarce shi da ya yi wani aikin. Bayan kammala aikin, Yusuf ya nemi ya ba shi kudi ya sayi abinci, amma a maimakon haka, sai sojan ya lakada masa duka har da shatin cizo a jikinsa.

Mahaifin yroki Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa, da Shugaban Hafsan Sojan Sama Air Marshal Hassan Abubakar da su tabbatar da cewa an musu adalci.

A nata bangaren, NAF, ta bakin Daraktan hulda da jama’a da yada labarai, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ta bayyana cewa, babban hafsan sojin sama, Hassan Abubakar, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi.

A cewar Gabkwet, marigayin ya samu sabani ne da wani sojan sama a kwanakin baya, wanda daga karshe aka sasanta su.

Gabkwet ya ce NAF ta himmatu wajen bankado gaskiyar rasuwar Shuaibu tare da mika ta’aziyya ga iyalansa.