
Rundunar sojin saman Nijeriya ta jibge dakarunta na musamman guda 150 a garin Nguroje, karamar hukumar Sardauna a jihar Taraba.
Babban hafsan sojin saman Nijeriya, Sadique Abubakar, wanda ya yijawabi wa dakarun a Jalingo kafin su tafi don kama aikinsu, ya jaddada musu cewa su nuna kwarewa wajen gudanar da akinsu.
Abubakar, wanda Napoleon Bali, daraktan ofireshin na rundunar yawakilce shi, ya ce: “Bari na yi amfani da wannan damar wajen jaddada bukatarku ta nuna kwarewa yayin gudanar da ayyukanku.
“Dole ku kiyaye dokokin aiki na rundunar sojin sama da dokoki yaki da kuma dokokin yaki da makami.
“Akwai bukatar ku kulla kyakkyawar alaka da mutanen wajen da za ku yi aiki yayin da su kuma za su tallafa muku wajen gudanar da ayyukanku.”
Jihar Taraba dai na daya daga cikin jahohin arewa maso tsakiya da kefama da rikice-rikicen manoma da makiyaya, wanda ya yi sanadiyyar hasarar rayuka.