Home Kanun Labarai Rundunar ‘yan sanda ta magantu kan sake kama Sanata Dino Melaye

Rundunar ‘yan sanda ta magantu kan sake kama Sanata Dino Melaye

0
Rundunar ‘yan sanda ta magantu kan sake kama Sanata Dino Melaye

Daga Hassan Y.A. Malik

Rundunar ‘an sandan ta bayyana cewa tuni dai ta cafke Dino Melaye a kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja domin ta mika shi gaban kotu a Lokoja, jihar Kogi, bisa zarginsa da hannu a muggan laifika da suka hada da hada kai wajen aikata laifi da kuma mallakar muggan makamai ba bisa ka’ida ba.

Shedikwatar rundunar ‘yan sandan Nijeriya ne ta saki sanarwa kan sake kama Sanata Dino Melaye ta bakin kakakinta, Jimoh Moshood.

 Ga kadan daga cikin sanarwar ta ‘yan sanda: “‘Yan sanda sun kama Sanata Dino Melaye a yau 2 ga watan Mayu, 2018 a farfajiyar kotun majistare da ke Wuse zone 2, Abuja bisa zarginsa da laifuka da suka hada da hadin gwiwa wajen aikata mugun laifi wanda hakan ya jawowa asarar wasu kadarorin gwamnati.

“Har ila yau, ‘yan sanda na zargin Sanata Dino da laifin yunkurin kashe kansa da kuma kokarin tserewa daga hannun ‘yan sanda.

“Kama Dino Melayen ya biyo bayan sallamarsa da babban asibi na kasa ya yi bayan da asibitin ya tabbatar ya samu lafiya yadda ya kamata, dalilin da ya sanya dole ya ci gaba da fuskantar zarge-zargen da a ke yi masa a kotu.

“In ba a manta ba dai, a ranar 24 ga watan Afrilu, 2018 da misalin karfe 12:00 na rana, Sanata Dino Melaye da ‘yan sandan Nijeriya suka cafke don gurfanar da shi a gaban kotun Lokoja, jihar Kogi, bisa laifin samunsa da mallakar muggan makamai da kuma hada kai wajen aikata babban laifi, amma sai wasu motoci kirar Hilux biyu dauke da ‘yan daba suka sha kan motar ‘yan sanda a lokacin da suke kokarin kai shi ofishinsu, lamarin da ya bawa Dino Melaye damar kokarin tserewa ta hanyar tsalle ya diro daga motar ‘yan sanda.

“‘Yan sanda za su gurfanar da Dino a gaban kotu a Lokoja ba tare da bata lokaci ba, don amsa laifukan da aka yi kararsa,” inji kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa.