
Babban Sufeton ‘yan-sandan Najeriya, Usman Alkali Baba ya bayar da umarnin hana amfani da lambar mota ta musamman ta tsaro wadda ake wa lakabi da SPY, a duk fadin kasar.
Umarnin ya biyo bayan irin matakan da shugaban ‘yan-sandan ke dauka na inganta tsaro da dakatar da yadda daidaikun mutane ke fakewa da wannan lambar mota su rika keta dokokin amfani da titi da sauran ka’idoji, kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar na kasa CSP Olumuyiwa Adejobi ta bayyana.
Sanarwar ta ce daga yanzu an haramta wa duk wata mota amfani da irin wannan lamba a ko’ina a fadin Najeriya.
Tare da umartar kwamishinonin ‘yan-sanda na jihohin kasar 36 da Abuja, da mataimakan sufeto janar na ‘yan sanda da su tabbatar da bin umarnin.
Jami’an fitattun mutane a Najeriya na amfani da lambar motar da sunan tsaroImage caption: Jami’an fitattun mutane a Najeriya na amfani da lambar motar da sunan tsaro.
Shugaban ‘yan-sandan ya kuma umarci duk ‘yan-sanda da sauran jami’an tsaro da ke aiki da manyan mutane masu amfani da motocin da ke da irin wannan lamba, su tabbatar da bin umarnin ko kuma su fuskanci hadarin kamasu kan kin bin umarnin.
Dokar ta bukaci a kwace dukkanin irin wannan lamba a ko’ina a kasar.