
Rahotanni na bayyana cewa a safiyar yau Lahadi Russia ta harba makami mai linzami a birnin Kyiv na Ukraine.
An ji ƙarar ababen fashewa a sassa daban-daban na birnin Kyiv ɗin.
Magajin birnin Vitali Klitshko, ya ce tuni motocin ɗaukar marasa lafiya haɗe da ma’aikatan ceto suka isa wurin.
Harin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaba Volodymyr Zelensky ya sake kira ga aminan Ukraine su kai musu ɗaukin makaman kare sararin samaniyar kasarsa.
A bidiyon da ya ke wallafa a kowanne dare tun bayan fara yaƙin, Mista Zelensky ya ce yaƙin da suke yi da Rasha ya shiga wani mataki mai sosa rai da tsananin wuya, bayan Rasha ta karɓe birnin Severodonetsk.