
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky zai yi wa ƴan majalisar Isra’ila jawabi ta kafar bidiyo, domin samun ƙarin goyon bayan kasashen duniya kan kutsen da Rasha ta yi wa kasarsa.
Wasu rahotanni na cewa zai yi amfani da damarsa ta zama Bayahude da faɗi tashin da suka yi, sannan ya kamanta halin da Ukraine ke ciki a hannun Russia, da neman goyon bayan yaƙarsu kwatankwacin wanda aka yi waƴan Nazi a lokacin yaƙin duniya na biyu.
Shugaba Zelensky ya yi magana da sauran ‘yan majalisu a sassa daban-daban na duniya ciki har da Birtaniya da Amirka, domin neman taimakonsu.
An bayyana cewa saboda gyaran da ake yi wa zauren Majalisar Isra’ila, za su yi tattaunawar ne a wani wuri mai cike da tsaro.