
Daga Muhammad Bashir Amin
Mune Matasa, mune Zamu kawo gyara ta hanyar amfani da ilimi da nutsuwa a cikin siyasa da sauran Al’amuran yau da Kullum.
Yana da kyau mu yi tattalin iliminmu da Nutsuwarmu da Hankalinmu da Mutuncinmu da mutane suke ganinmu da su. Kada mu zubar da Ni’mar da Allah ya yi mana saboda Siyasar wannan zamanin ta hanyar zage-zage da cin zarafin juna ba bisa hakkin Shari’a ba.
Ya sau da dama mukan yi amfani da wannan damar ta amfani da facebook ta hanyar da bata dace ba, wurin cin zarafin junanmu ba tare da la’akari da cewa Mutanen kirki nagartattu na biye damu sunan kallonmu ba.
Daga cikin masu biye damu a shafinmu na facebook akwai Iyayenmu da Malamanmu na Addini dana boko da Surukanmu da abokanan huldarmu ta rayuwar yau-da-kullum, amma sai kaga mutum ya rufe idonsa yana ta zuba futsara ba ji ba gani.
Wani abin takaicinma shi ne; muna mantawa da Mutuwa, muna mantawa ba wanda ake fadawa lokacin da zai mutu kafin mutuwarsa ballantana ya yi maza ya gyara mummunan aikinsa kafin ya koma zuwa ga Mahaliccinsa.
Akwai wani Abu da hukumar facebook ta kirkiro da shi da koyaushe yake tunatar dani Ranar Alkiyama. Wannan abin shi ne “Memories” wato tuna maka tsohon rubutunka da zarar ya dauki Shekara ko Shekarau idan kwanan watan ranar da ka yi rubutun ya zago. Idan ka yi rubutu ko sanya hoto mai tarbiyya ko Sharri haka za a hasko maka shi kai da abokanka dake facebook.
Abin tsoran shi ne, idan watarana kana raye aka nuna maka ‘memories’ idan rashin tarbiyya ka rubuta ko hotan batsa ka samu damar gogewa, to fa baka da tabbas cewa duk Shekara zaka gani ka samu irin wannan damar.
Lallai mu Kwana da sanin duk abinda muke rubutawa ko sakawa a facebook page ko social media ba mu ci bilis ba, Akwai ranar bita, ranar bitar nan kuma ita ce ranar Alkiyama.
Ina yi wa kaina da ‘yan uwa da abokan arziki Nasiha lallai mu kiyaye furucinmu da abinda muke rubutawa saboda Akwai ranar bitar labarai. Allah ka shirye mu, ka gyara mana Ayyukanmu.