
A yau ne sabuwar ministar kudi ta tarayyar Najeriya Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta kama aiki a sabuwar ma’aikatar kudi da aka tura ya a matsayin babbar minista.
Zainab Ahmed ya kama aiki ne bayan da tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun tayi murabus bayan da wata jarida ta bankado badakalar yin jabun takardun kammala hidimar kasa a Najeriya.
Bayanai sun tabbatar da cewar tuni tsohuwar Ministar Kemi Adeosun ta har Najeriya zuwa kasar Burtaniya inda daman a can aka haifeta kuma tayi karatu.