Home Labarai Sabuwar shekarar Musulunci: A fara duban watan Muharram daga gobe Alhamis — Sultan

Sabuwar shekarar Musulunci: A fara duban watan Muharram daga gobe Alhamis — Sultan

0
Sabuwar shekarar Musulunci: A fara duban watan Muharram daga gobe Alhamis — Sultan

 

 

Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, a yau Laraba ya umurci Musulmi da su fara duban jinjirin watan Muharram daga gobe Alhamis.

Ganin jinjirin watan, a kalandar Hijira, yana nuna sabuwar shekara ta Musulunci ta 1444H.

Abubakar, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Ƙasa, NSCIA, ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin ba da shawara kan harkokin addini a Sakkwato.

“ana sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Alhamis 28 ga watan Yuli, daidai da 29 ga Zul-Hijjah 1443AH ita ce ranar da za a duba jinjirin watan Al-Muharram 1444AH.

“Saboda haka, an bukaci musulmai da su fara neman jinjirin wata a ranar Alhamis kuma su kai rahoto ga gunduma ko kauye mafi kusa don tuntubar Sarkin Musulmi,” “in ji shi.