
Wata babbar kotu a kasar Malaysiya a ranar Alhamis ta yankewa wasu dalibai ‘yan Najeriya hukuncin kisa, bayan da ta same su da laifin safarar kwayar da ta kai kilogiram 3.5, kimanin shekaru uku da suka gabata.
Alkalin kotun Datuk Abdul Halim, shi ya bayar da hukuncin, bayan binciken kwakwaf da kotun tayi, sanna ta saurari dukkan bangaroro, ta samu Mustapha Azmir dan shekau 28 da kua Jude Nnamdi Achonye dan shekaru 30 da laifi, ta kuma zartar musu da hukunci.
Tun farko dai, an gurfanar da Mustapfa da Achonye da bisa zargin yin safarar miyagun kwayoyi, a ranar 2 ga watan Satumbar 2014 da misalin karfe 3 da rabi na yamma. Laifin da ya sabawa sashi na 39B karamin kashi na 1 cikin baka (a) kundin mulkin kasar ta Malaysiya na shekarar 1952 wanda yayi haramci kan tamuli da miyagun kwayoyi.
A bisa binciken kotu, daliban wadan da suke karatu a makarantu masu zaman kansu a birnin Kuwala Lumpur, ‘yan sanda sun kame daliban biyu ne,lokacin da aka aiko musu da wasu akwatuna da suke dauke da miyagun kwayoyi daga wani kamfani a sashin da suke zaman haya.
Alkali Abdul Halim, a lokacin da yake bayyana hukuncin, sai da ya gama sauraren shaidu 23 da kuma masu bayar da kari ga wadan da ake zargi, bayan da aka gabatar da shaida guda 73 da take tabbatar da mutanan sun aikata laifin dumu-dumu.
“Lauyan wadan da ake tuhumar ya gaza gamsar da alkalin da kwararan shaidun da zasu tabbatarwa da kotun mutanan da ake zargin basu aikata laifin ba, duk kuwa da cewar, daliban sun musanta laifin da ake tuhumarsu da shi”
Mataimakin mai shigar da kara na Gwamnati ne ya tsaya a kotun a madadin masu gabatar da kara, yayin da lauyan wadan da ake zargi Leonard Anselm Gomes ya bayyana a kotun a madadinsu.