Home Labarai Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti ya yi murabus

Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti ya yi murabus

0
Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti ya yi murabus

 

 

Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti, Biodun Oyebanji ya yi murabus, kamar yadda Kanfanin Daillancin Labarai, NAN ya rawaito.

Yinka Oyebode, Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya baiyana cewa gwamnan ya amince da murabus din na Oyebanji.

Oyebode ya ce murabus ɗin na Sakataren gwamnatin na ƙunshe ne a wata wasiƙa da ya rubutawa gwamnan a ranar 3 ga watan Disamba, inda ta fara aiki a ranar Talata, 7 ga Disamba.

Oyebode ya ƙara da cewa, a cikin wasiƙar, Oyebanji ya shaidawa gwamnan cewa yana son tsayawa takarar gwamna ne shi ya sa ya ajiye aikinsa.

“Da ya ke rubuta amsar wasiƙar, gwamna Fayemi ya godewa Oyebanji a bisa gudunmawar da ya baiwa gwamnatin tun sanda a ka kafa ta a 2018.

“Sannan ya yi masa fatan alheri da nasara a abubuwan da ya sa gaba a rayuwa,” in ji Oyebode.