
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce an kai hari ofishinta da ke karamar hukumar Orlu a jihar Imo da ake gyara wa a ranar Alhamis.
INEC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zaɓe, Festus Okoye ya fitar a jiya Juma’a a Abuja.
Okoye ya ce, kwamishiniyar zabe (REC) reshen jihar Imo, Farfesa Sylvia Agu, ta ruwaito cewa an kai hari ofishin hukumar da ke Orlu.
“Al’amarin ya faru ne a ranar Alhamis, 1 ga Disamba, 2022.
“Ginin, wanda ake tsaka da gyaran sa biyo bayan harin da aka kai a baya, an sake lalata shi kuma an kone wasu sassa na sa,”
Okoye ya ce an sace uku daga cikin ma’aikatan da ke gyaran su bakwai an yi garkuwa da su, amma daga baya aka sake su.
“Da ma barnar ta fi haka girma in banda zuwan ƴan sanda wajen da gaggawa.
“Wannan hari ne ɗaya daga cikin da yawa da a ke kai wa.
“Hukumar ta sake bayyana damuwarta kan yawaitar hare-haren da ake kai wa cibiyoyinta da kuma illar da ke tattare da shirye-shiryenmu na zaben 2023.