
Hukumar dake yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta sake rubanya laifukan da ake cajin tsohon mai baiwa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki, daga laifuka 19 zuwa 32 da ake tuhumarsa da su dake da aaka da badakalar biliyoyin kudade.
Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Sambo Dasuki da wasu mutum uku agaban wata babbar kotu dake Maitama a Abuja, inda ake zarginsu da wadaka da kuma sama da fadi da zunzurutun kudin da ya kai Naira biliyan 33.3 dagalalitar Gwamnati.
Idan za’a iya tunawa tun a watan Nuwambar 2015 ne, hukumar EFCC ta kame tsohon mai baiwa tsohon SHugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Sambo Dasuki akan almundahanar makudan kudaden Gwamnati.
An sake gurfanar da Sambo Dasuki ne tare da Shuaibu Salisu tsohon Daraktan dake lura da ayyuka da sha’anin kudade na ofishin Mai baiwa Shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, dakuma tsohon janar manaja na kamfanin mai na kasa NNPC Aminu Baba-Kusa da kuma wasu kamfanoni guda biyu.
A lokacin zaman kotun an karantawa mutanen da ake zargi sabbin laifukan da ake cajinsu da su guda 32 inda dukkansu suka amsa cewar basu aikata laifukan da ake tuhumarsu da su ba.
Alkalin kotun ya dage zaman kotun zuwa ranar 2 zuwa 5 ga watan Yulin wannan shekarar.