
Ƴan bindigar da su ka kai hari kan jirgin kasar da ke kan hanyar Kaduna-Abuja sun sako ƙarin mutane bakwai bayan sama da kwanaki 100 da garkuwa da su.
‘Yan bindigar sun sako mutanen bakwan ne sa’o’i kaɗan da cikar wa’adin kwanaki biyu da su ka bayar na fara yanka mutanen da su ka sace.
Daga cikin mutanen bakwai da ‘yan bindigar su ka saki akwai Dr. Muhammad Abuzar wani dan kasar Pakistan, da wata mace ɗaya mai suna Bosede Olurotimi.
Sauran wadanda aka sakin sun hada da Sadiq Abdullahi dan tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello kuma shugaban kungiyar dattawan arewacin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi, da Aliyu Usman, da Abubakar Zubairu, da Alhassan Sule, da kuma Daiyabu Paki Tsohon shugaban karamar hukumar Ikara kuma shugaban wata hukuma a jihar Kaduna.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a kwanakin baya ne dai ƴan ta’addan su ka sami mutum 11 da ga cikin su.