
Sanata Dino Melaye dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, wanda jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasa suka kama ranar Litinin a filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja, ya samu ‘yanci, inda aka sake shi bayan da ya shafe sa’o’i biyu a hannun jami’an NIS.
Mai magana da yawun Sanatan, Gideon Ayodele ya tabbatar da cewar an saki mai gidan nasa, bayan da aka tsare shi dazu da safe a filin jirgin saman Abuja,akan hanyarsa ta zuwa kasar Maroko.