Home Labarai Sakin Nnamdi Kanu zai maida Nijeriya ƙasar da ba doka kwata-kwata, CNG ta gargaɗi Buhari

Sakin Nnamdi Kanu zai maida Nijeriya ƙasar da ba doka kwata-kwata, CNG ta gargaɗi Buhari

0
Sakin Nnamdi Kanu zai maida Nijeriya ƙasar da ba doka kwata-kwata, CNG ta gargaɗi Buhari

Gamaiyar Ƙungiyoyin kare yankin Arewacin Najeriya, CNG ta ce idan har Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sake ya saki Jagoran Haramtacciyar Ƙungiyar Ƴan ta’adda ta IPOB,Nnamdi Kanu, to kasar za ta kasance cikin halin rashin doka da oda kwata-kwata.

A makon da ya gabata ne dai wasu shugabannin inyamirai, a ƙarƙashin jagorancin Mbazulike Amaechi su ka ziyarci Buhari a fadar shugaban ƙasa, in da su ka nemi da ya saki Kanu.

Da ya ke maida martani game da buƙatar inyamiran, sai Buhari ya ce gaskiya buƙatar su mai matuƙar wahala ce domin batun na Kanu ya na gaban kotu, amma dai zai duba ya ga yiwuwar cika musu buƙatar ta su.

To amma wannan amsa ta Buhari ba ta yiwa ƙungiyar CNG daɗi ba, inda ta ce to za ta ɗora laifin kashe ƴan arewa da Kanu ya sa a ka yi idan har shugaban ƙasar ya saki Kanu ɗin.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta yi a Kano ranar Litinin, CNG, ta bakin Kakakin ta, Abdul-Azeez Suleiman ta tuna cewa tun daga shekara 2017 zuwa 2020 Kanu ya ke aikata ta’asa a kan ƴan arewa.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa” Kanu ya sa yaransa sun kashe mutane da dama da su ka haɗa da jami’an tsaro sama da 400 da kuma sauran al’umma, musamman yan arewa,”

“Saboda haka idan har Buhari ya biye ta tasu to lallai ƙasar nan za ta zama ba doka da oda kwata-kwata, inda kowa ma sai ya fito ya ce zai zama ɗan ta’adda.

“Idan har Buhari ya saki Kanu, to za mu rike shi da lefin zubar da jinin ƴan arewa. Saboda haka kada ya sake ya biye ta tasu,”

CNG ta yi kira ga Buhari da ya tabbatar da kama da kuma hukunta su waɗan nan inyamiran da su ka je masa da bukatar ya saki Kanu, da ma wasu wadanda da yawunsu su ka je fadar.