
Kafin ku halacci wajen zabe yakamata kuyi karatun ta nutsu, ku guji gaggawa ku tsaya ku duba yan takara, ku guji karbar kudi don shike jefa kasa cikin masifa.
An dade ana rabawa Delegate kudi a duk jamiyyun Nigeria amma bama samun biyan bukata, don haka yakamata mu gwada cancanta a wannan karon.
-Shin wanene zai iya mana maganin rashin tsaro a Nigeria?
– Shin wanene zai iya dawo da hadin kan yan’Nigeria wanda iyayenmu su Sardauna, Awolowo, Tafawa Balewa da Zik suka zauna akai?
– Shin wanene zai iya dawo mana da masana’antu don maganin rashin aikin yi ga matasan mu?
– Shin wanene ya san tarihin Nigeria ciki da waje?
– Waye yasan tarihin PDP , yasan manufofin PDP, ya zauna a PDP tun kafuwarta yake mata hidima ba dare ba rana ba ruwa ba iska, wuya da dadi bai taba barin PDP ba daidai da sa’a daya?
-Shin wanene zai dawo mana da bin dokokin kasa batare da amfani da hukumomin tsaro ba don cin mutuncin abokan hamayya ba? Waye zai dawo mana da bin doka da oda ?
– Wanene yayi mulki a Jiharsa ya mayar da jihar daga abin tausayi da dariya zuwa abin alfahari?
– Wanene tun farkon fara siyasarsa zuwa yau ba’a taba samunsa da laifin nuna kabilanci ko jinsi ba?
– Wanene yan’takara yayi ministan hulda da kasashen duniya, yasan duniya kuma tuniya ta sanshi?
– Wanene yake cikin mutum tara da aka kafa Jamiyyar PDP dashi?
– Wanene ya fara ganawa da shugabannin PDP na jihohin Nigeria kafin fitowarsa takara?
– Wanene ya ziyarci Jihohin Nigeria daya bayan daya a ciki harda Borno, Yobe, Zamfara, Benue, Ebonyi, da sauran jihohin da ake samun matsalolin rashin tsaro?
– Shin wanene ake masa lakabi da jagoran talakawa saboda kusancinsa da talakawa?
Kusani fa yan’ Nigeria suna kallonku sun zuba muku ido su gani ko jam’iyyar PDP tayi karatun ta nutsu ko batayi ba? Ko jamiyyar PDP tayi hankali ko batayiba? Ko jamiyyar PDP tayi niyyar karbar mulki a hannun APC ko batayiba ?
Muddin aka samu rashin adalchi wajen fitar da dan takarar shugaban kasa ba , muddin akayi kokarin hana talakawa bukatarsu ko akayi kokarin fifita bako akan dan gida babu shakka baza a samu biyan bukata ba.
IDAN KUNNE YAJI, JIKI YA TSIRA