Home Labarai Sallah: Ƴan sanda sun kama ƴan daba 84 a Kano

Sallah: Ƴan sanda sun kama ƴan daba 84 a Kano

0
Sallah: Ƴan sanda sun kama ƴan daba 84 a Kano

 

 

Rundunar Ƴan Sanda ta ƙasa, reshen jihar Kano tace ta samu nasarar kama ƴan daba 84 da muggan makamai a yayin bukukuwan Babbar Sallah a faɗin jihar.

Kwamishinan Ƴan sanda na jihar Kano, Samaila Shu’aibu Dikko ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Juma’a a Kano.

Sanarwar ta ce an kama ƴan daban ne a dukka masarautu biyar na jihar a yayin bukukuwan Sallah.

Kiyawa ya ƙara da cewa ƴan daban sun shiga hannu ne a ranakun Hawan Daushe da Hawan Nasarawa da Hawan Dorayi da sauran haye-hayen Sallah da aka yi a sauran masarautun jihar.

A sanarwar, kwamishinan ya yabawa al’ummar jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro bisa gudunmawar da su ka bayar har aka samu gagarumar nasara a yayin bukukuwan Babbar Sallah.

Ya kuma kara da cewa za a iya tuntuɓar rundunar domin kiran gaggawa a kan waɗannan lambobin waya: 08032419754, 08123821575, 08076091271 da kuma 09029292926.