Home Labarai An sallami Osinbajo daga asibiti

An sallami Osinbajo daga asibiti

0
An sallami Osinbajo daga asibiti

 

An sallami Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo daga asibiti bayan an yi masa aiki a ƙafarsa.

Babban liktia na musamman na mataimakin shugaban kasar, Nicholas Audifferen ne ya shaida haka.

Kakakin Osonbajo ɗin, Laolu Akande ne ya fadi ta bakin Audifferen a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.

Ya ce an sallami Osinbajo ɗin ne bayan an yi masa aiki lafiya lau a asibitin Duchess International Hospital da ke Legas.

Ya ƙara da cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ɗin ya shafe mako daya. Asibitin kafin a sallame shi, inda ya ce yana samun sauki sosai.