Home Siyasa Sama da manoman shinkafa miliyan ɗaya sun nuna goyon bayansu ga Atiku a 2023

Sama da manoman shinkafa miliyan ɗaya sun nuna goyon bayansu ga Atiku a 2023

0
Sama da manoman shinkafa miliyan ɗaya sun nuna goyon bayansu ga Atiku a 2023

 

 

 

Manoman shinkafa na ƙasa, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Manoman shinkafa, sarrafa ta da kuma Kasuwancin ta, NARPPMMAN, sama da miliyan ɗaya ne su ka nuna goyon bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar a zaɓen 2023.

Ƴan kungiyar ɗau wannan alkawari ne yayin da su kai wa Atiku ziyarar goyon baya a gidansa da ke Abuja a jihar Asabar.

A wata sanarwar da Mataimakin Atiku na Musamman kan kafafen yaɗa labarai, Abdulrasheed Shehu ya fitar a yau Lahadi, manoman sun ce sun kawo masa ziyarar ne domin taya shi murnar samun tikitin takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar PDP.

Jagoran tawagar, Alhaji Ahmadu Mustapha ya yi alkawarin cewar kungiyar zata mara baya tare da kasancewa masu biyayya ga dan takarar.

A cewar sa, mambobin kungiyar sama da miliyan ɗaya sun yanke shawarar marar baya ga Atiku sabo da yadda yake zuba jari a ɓangaren noma, inda suka ce sun gamsu Atiku shima manomin shinkafa ne.

A nasa jawabin, tsohon mataimakin shugaban kasar ya godewa kungiyar bisa wannan ziyara, inda ya ce tun 1984 ya shiga harkar noma tun ma kafin a kafa wannan kungiyar.

“Ɗan Takarar shugabancin kasar na Jam’iyyar PDP yace idan aka zabe shi shugaban kasa, zai ƙara ruɓanya ƙoƙarin bunƙasa harkokin noma, saboda muhimmancin sa ga kasa.

“ya yi alkawarin bada tallafi ga manoma domin habaka amfanin gonar da suke samu. Kazalika, ya yi alkawarin Samar da tsarin tattaunawa akai-akai da manoman domin karfafa giwar sanya jari don riba a bangaren,” in ji sanarwar.