
Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta ce sama da mutane 700,000 ne ke kashe kansu a duk shekara a faɗin duniya, inda kashi 77 cikin 100 na kashe-kashen na duniya ke faruwa a kasashe masu karamin karfi da matsakaita.
Wakilin WHO a Najeriya, Walter Kazadi Mulombo ne ya bayyana hakan a jiya Lahadi cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin ranar rigakafin kashe kai ta duniya ta bana.
A cewarsa, ga kowane kashe kai, akwai yiwuwar wasu mutane 20 da ke yin yunƙurin kashe kansu kuma da yawa suna da tunanin kashe kan na su.
Ya ce: “Kisan kai shi ne na huɗu da ke haddasa mace-mace tsakanin ‘yan shekara 15-29. Duk wani lamari na kashe kai bala’i ne da ya shafi iyalai da al’ummomi da kuma ɗaukacin ƙasar, kuma yana da tasiri mai dorewa a kan mutanen da aka bari a baya.”
Mulombo ya ce ana iya magance kashe kai ta hanyar lokaci, ganin yunkurik kisan da ido da kuma hanyoyin kariya marasa cin kuɗi.