Home Kasuwanci Sama da ƴan Nijeriya 2,000 ke rububin guraben aiki 280 a bajakolin aiki na Huawei

Sama da ƴan Nijeriya 2,000 ke rububin guraben aiki 280 a bajakolin aiki na Huawei

0
Sama da ƴan Nijeriya 2,000 ke rububin guraben aiki 280 a bajakolin aiki na Huawei

 

 

Sama da matasa ƴan Nijeriya 2,000 ne su ka yi rububin neman guraben aiki 280 a bajakolin aiki na kamfanin Huawei da a ka yi a Abuja.

Kamfanin Huawei, wanda ya ke na gaba a wajen harkar sadarwa na shirya taron, wanda sama da kasashe 170 a faɗin duniya su ka halarta a jiya Laraba.

Matasan, waɗanda su ka fito da ga sassa daban-daban, sun rarraba takardunsu na neman aiki ga kamfanunuwa daban-daban da su ka zo yin bajakolin.

Haka kuma wasu daga cikin masu neman aikin tun a wajen a ka yi musu tambayoyin daukar aiki.

Osita Nweze, Mataimakin Manajan-Darakta na Huawei ɓangaren tsaron yanar gizo, wanda ya wakilci Manajan-Darakta din, ya baiyana aniyar kamfanin wajen bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya.

Ya ce ɗaya daga cikin manufofin kamfanin shine rage yawan tashin aikin yi ta hanyar kirkiro da ayyukan yi a ƙasar.