
Okeke Anya, Manajan Shirye-Shirye na Cibiyar Wayar da kai da Shawarwari ga Al’umma, CISLAC, ya ce a ƙalla ƴan Nijeriya 16,000 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon cututtuka masu alaƙa da taba.
Anya, wanda ya bayyana hakan a wani taro da aka yi a birnin Calabar a yau Litinin domin ƙarfafa dokar yaƙi da shan taba da kuma dokar kula da harajin taba a Cross River, ya ƙara da cewa a duk shekara ana asarar rayuka miliyan 8 a duniya sakamakon irin waɗannan cututtuka.
Ya nuna damuwarsa cewa idan ba a yi komai ba, illar taba za ta ci gaba da ƙaruwa.
Ya ce a cikin shekaru biyu da su ka gabata, CISLAC ta na gudanar da shirye-shirye na inganta yadda za a taimaka wa mutane su fahimci asarar da taba ke haifar wa, musamman ta fuskar haraji.
Ya kara da cewa, maƙasudin abin da ya sa su ke wayar da kan al’umma bai wuce sabo da irin mummunar illar taba cigari ga rayuwar ɗan adam ba.