
Daga Hassan Y.A. Malik
Shugaban hukumar inganta harkar lafiya a jihar Bauchi, Adamu Gamawa, ya tabbatar da barkewar cutar amai da gudawa a jihar.
Ya ce mutane 20 ne izuwa yanzu suka kamu da cutar, a ciki 2 sun rasa rayukan su.
Gamawa ya fadi haka ne a yayin da ya ke magana da manema labarai a ranar Litinin da ta gabata, inda ya ce tuni sun dauki matakai kwarara da za su tabbatar cutar ba ta ci gaba da yaduwa ba.
A jiya Talata kuma, Gamawa ya sanar da mutuwar mutane 3 a sakamakon kamuwa da suka yi da cutar zazzabin Lassa a jahar.
Ya ce an samu kimanin mutane 25 dauke da cutar a kananan hukumomi 7 na jahar, wanda suka hada da Alkaleri da Bauchi da Bogoro da Dass da Tafawa Balewa da Toro da Warji.
Ya ce an samu mutane 25 din ne a tsakanin 1 ga watan Janairu da 4 ga watan Maris na shekarar nan.