
Fitaccen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke, wanda a ka fi sani da Davido ya baiyana cewa ya samu kuɗi wuri na gugar wuri har dala miliyan 22.3 a shekarar 2021 da mu ka yi bankwana da ita.
A jiya Juma’a ne mawaƙin, wanda ya ke da alaƙa da mawaƙan Amurka, ya baiyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na kafar sadarwa.
“Na samu dala miliyan 22.3 a wannan shekarar,” in ji Davido.
Ƙimar kuɗin ta kai naira biliyan 13 a kuɗin Nijeriya.