Home Lafiya An samu masu tarin fuka 4,506 a watanni 5 a Kaduna

An samu masu tarin fuka 4,506 a watanni 5 a Kaduna

0
An samu masu tarin fuka 4,506 a watanni 5 a Kaduna

 

 

An samu masu tarin fuka, TB, 4,506 a Jihar Kaduna, kamar yadda Shirin Yaƙi da cutar tarin fuka, Kuturta da kuma Ciwon Buruli a Jihar Kaduna ya bayyana a yau Talata.

Manajan shirin na jiha, Dakta Sadiq Idris ya bayyana haka ga manema labarai a Kaduna.

“Wannan na nuni da cewa an samu ƙaruwar kashi 114 idan aka kwatanta da binciken cutar tarin fuka na zangon farko na 2021,” in ji shi.

Ya ce shirin ya fadada ayyukansa a jihar zuwa cibiyoyin jinya 976, inda ya ƙara da cewa an baiwa dukkan marasa lafiya magani kyauta.

“Waɗannan cibiyoyi sun haɗa da dukkanin manyan asibitoci 31, cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko 672, cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu 222, wuraren ibada 48 da manyan cibiyoyin ilimi guda uku (kashi 68 cikin 100 na kayan aiki) a jihar.

“Gwamnatin jihar ta kuma samar da manyan motocin daukar marasa lafiya guda biyar sanye da injinan ɗaukar hoton sassan jiki, wato X-ray na na’urar zamani da na’urori masu launi guda 10 don tantance cutar tarin fuka, COVID-19 da sauran cututtuka daban-daban a cikin al’ummomin a jihar.

“Wannan ko shakka babu zai kara yawan binciken cutar tarin fuka a jihar,” in ji Idris.